Connect with us

Labaran Kano

Cutar Kyanda: Za ayi wa yara miliyan 2 rigakafi a kano

Published

on


Gwamnatin jihar Kano ta ce za a yiwa yara sama da miliyan biyu rigakafin kyanda a faɗin jihar.

Kwamishinan Lafiya Dakta Kabiru Ibrahim Tsanyawa ne ya bayyana hakan a taron manema labarai.

Ya ce za a fara rigakafin cutar ne daga ranar 22 zuwa 28 ga watan nan na Nuwamba.

Dakta Tsanyawa ya ƙara da cewa yara da dama ne ke mutuwa sanadiyyar kamuwa da cutar, wanda hakan ya sanya yin rigakafin kyauta a dukkan shiyyoyin lafiya da kuma masarautun jihar ta Kano.

Kwamishinan ya ce gwamnati ta ware sama da Naira Miliyan ashirin da biyu domin yin rigakafin ga yara ƴan ƙasa da shekaru biyar a jihar.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a Reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Freedom Radio Dutse 99.5 FM Dala FM Kano 88.5

Now Streaming

Archives

Copyright © 2019. Freedom Radio Group. All Rights Reserved.

error: Content is protected !!