Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Da ɗumi-ɗumi: An naɗa sabon mataimakin shugaban majalisar dokoki

Published

on

Ɗan majalisar dokokin Kano mai wakiltar ƙaramar hukumar Ƙiru Kabiru Hassan Dashi ya zama sabon mataimakin shugaban majalisar dokoki.

Hakan ya biyo bayan ajiye muƙamin da tsohon mataimakin shugaban majalisar Alhaji Zubairu Hamza Massu mai wakiltar ƙaramar hukumar Sumaila ya yi.

Yayin zaman majalisar na yau Litinin shugaban majalisar Injiniya Hamisu Ibrahim Chidari, ya karanta wasiƙar da Massu ya aikewa majalisar inda kuma nan take aka ayyana kujerar a matsayin wadda babu kowa a kanta.

Daga nan ne kuma aka bada damar zaɓar wanda zai hau kujerar inda kuma ɗan majalisa mai wakiltar ƙaramar hukumar Dawakin Tofa Sale Ahmad Marke ya zaɓi ɗan majalisar na Ƙiru, kuma ƙudurin ya samu goyon bayan ɗan majalisa mai wakiltar Wudil Alhaji Nuhu Abdullahi Achika.

Hakan ne ya baiwa Kabiru Hassan Dashi damar samun nasarar zama mataimakin shugaban majalisar bayan da mambobi 28 suka amince da zaɓar tasa.

Wakilin Freedom Radio Auwal Hassan Fagge ya ruwaito cewa bayan samun goyon ɗaukacin mambobin majalisar ne kuma aka rantsar da shi wanda muƙamin nasa ya fara aiki nan take.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!