Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Da ɗumi-ɗumi – An tsige shugaban majalisar dokoki da mataimakin sa a Kebbi

Published

on

Majalisar dokokin jihar Kebbi ta tsige shugaban majalisar Abdulmumeen Kamba da mataimakinsa Alhaji Muhammad Buhari-Aleiro.

Shugaban kwamitin yada labarai da al’adu na majalisar, Alhaji Muhammad Tukur ne ya sanar da tsigewar bayan zaman majalisar na sirri.

Ya ce nan take aka maye gurbin shugaban da mataimakin mai tsawatarwa Muhammad Abubakar Lolo yayin da aka maye gurbin mataimakin shugaban majalisar da Muhammad Usman.

Tukur, bai bayyana dalilin tsige shugabannin ba, sai dai ya ce, mambobin majalisar 20 cikin 24 sun halarci zaman.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!