Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Kiwon Lafiya

Da ɗumi-ɗumi: manyan mataimakan shugaba Buhari sun kamu da cutar corona

Published

on

Wasu daga cikin ministoci da mataimakan shugaban ƙasa Muhammadu Buhari sun kamu da cutar corona.

Cikin waɗanda suka kamu da cutar sun haɗa da ministan yaɗa labarai da raya al’adu Alhaji Lai Muhammad da babban sakataren fadar shugaban ƙasa Tijjani Umar.

Sai Yusuf Dodo da babban jami’in tsaronsa Aliyu Musa sai kuma mai taimaka masa kan kafofin yaɗa labarai Malam Garba Shehu.

Jaridar Premium Times ta rawaito cewa bayan yi musu gwajin corona sakamakon ya tabbatar da sun kamu da kwayar cutar.

Sai dai ana tsammanin cutar bata yi musu tsanani ba kasancewar sun karɓi cikakkiyar allurar rigakafin cutar Corona.

Idan dai za a iya tunawa, a kwanakin baya ne uwargidan shugaban ƙasa HajiyaA’isha Muhammadu Buhari da maigidanta suka dawo daga birnin Istanbul na ƙasar Turkiya, inda kuma ta ba da umarnin rufe ofishinta tare da umurtar ma’aikatanta da su zauna a gida na wani lokaci.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!