Labarai
Da ɗumi-ɗumi: Kotu ta yanke hukunci ga ƴan sandan da suka hallaka wani matashi a Kano
Kotu ta umarci wasu ƴan sanda biyu a Kano da su biya diyyar miliyan 50 ga iyalan wani matashi da suka yi sanadiyyar ajalinsa.
Babbar kotun jihar Kano mai lamba 4 da ke Sakatariyar Audu Baƙo ta yanke wa wasu ƴan sanda biyu hukuncin biyan diyyar miliyan 50 ga iyayen wani matashi.
Kotu ta samu ƴan sandan biyu Sufeto Uba Bangajiya da Insfekta Garba Galadima waɗanda ke aiki a sashen ƴan sanda na SARS da ke Kano, wanda aka rushe, da hallaka wani matashi Mustapha Idris Muhammad mazaunin unguwar Sheka.
Ƴan sanda sun kama shi inda suka zarge shi da yin fashi, a kan hakan ne suka tsare shi, sannan suka riƙa lakaɗa masa duka har sai da ya rasa ransa.
Labarai masu alaƙa:
Ba za mu dawo da ƴan sandan SARS ba – IG Alƙali Baba
Za a ɗauki sabbin ƴan sanda dubu 60 a Najeriya
A wancan lokaci dai shirin Inda Ranka na Freedom Radio ne, ya yayata labarin, abin da ya kai ga lauyan nan Barista Abba Hikima Fagge ya shigar da ƙara a gaban kotu.
Yayin zaman kotun na yau mai shari’a Yusuf Muhammad Ubale ya umarci ƴan sandan su biya diyyar miliyan 50 ga iyayen marigayin, sannan su shiga kafafen yaɗa labarai su nemi afuwar danginsa nan take.
Wakilinmu Bashir Muhammad Inuwa ya rawaito cewa, alƙalin ya kuma umarci ƴan sandan da su dawo da wayar marigayin ƙirar VIVO da ke wajensu.
You must be logged in to post a comment Login