Labarai
Da ɗumi-ɗumi: ‘Yan sanda sun kama DCP Abba Kyari
Rundunar ‘yan sandan Najeriya ta kama dakataccen kwamandan sashin binciken miyagun Laifuka da ke ƙarƙashin ofishin sufeto janar na ƴan sanda DCP Abba Kyari.
Jaridar PUNCH ta rawaito cewa an kama shi ne tare da wasu mutane huɗu a ranar Litinin.
Kamen nasa na zuwa ne sa’o’i kaɗan bayan da hukumar yaƙi da fataucin miyagun ƙwayoyi ta ƙasa NDLEA ta bayyana cewa y’tana neman sa ruwa a jallo bisa zargin alaƙa da masu safar miyagun ƙwayoyi zuwa Najeriya.
You must be logged in to post a comment Login