Labaran Kano
Da dumi-dumin sa- Wasu likitoci sun rasu bayan yiwa wata mace tiyata
Likitoci 2 sun rasu Jim kadan Bayan yiwa wata marar lafiya tiyata a asibitin koyarwa na Malam Aminu Kano.
Daga bisani galiban ma aikata da suka taimaka wajen yiwa marar lafiyar tiyata sun kamu da wani zazzafan zazzabi wanda har yanzu aka kasa Gano kansa.
Wannan dai yasa an fara zargin yiwuwar samun barkewar zazzabin Lassa, Koda yake mahukuntan asibitin na Malam Aminu Kano sunce sun aika da jinin wadanda ake zargin sun yi mu’amalla da marar lafiyar wacce tuni itama ta rasu, zuwa Lagos domin yin gwaji a tabbatar da matsayin irin wannan zazzabin da ake zargin na Lassa ne.
Dan haka ake kira ga al’umma da su kiyaye tsaftar muhalli.