Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Da gaske da kyar na sha ba wasan kwaikwayo na shirya ba – Gwamnan Benue

Published

on

Gwamnan jihar Benue Samuel Ortom ya musanta zargin da ake yi masa na cewa, ya tsara wasan kwaikwayo ne game da batun ikirarin da ya yi na cewa, ‘yan bindiga sun kai wa jerin gwanon motocinsa hari a kauyen Tyomu da ke kan titin Gboko zuwa Makurdi.

A yayin zantawa da ‘yan jaridu bayan gudanar da wani taron sirri da shugaba Buhari a fadar Asorok, Samuel Ortom ya ce zancen cewa shi da kansa ya tsara harin, tsoki burutsu ne kawai.

A cewar sa, zai yi matukar wuya ace ya tsara hari domin kuwa a cikin jami’an tsaro da ke kula da lafiyarsa, akwai Hausawa, Fulani da kuma Yarbawa da ma sauran wasu yaruka na daban.

‘‘Ni fa na fi son in bar batun da muka tattauna tsakani na da shi (shugaban kasa). Ya yadda da abin da ya faru dani kuma ya bani shawara kan abin da ya kamata inyi. Sannan suma jami’an tsaro suna aikin su, saboda haka ban damu da abin da jama’a ke cewa ba’’ a cewar gwamnan.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!