Labarai
Daga ƙarshe dai: An sulhunta tsakanin gwamnati da matuƙa adaidaita sahu
Ƙungiyar matuƙa babura masu ƙafa uku sun janye yajin aikin da suka shafe kwanaki uku suna yi.
Janye yajin aikin dai ya biyo bayan doguwar tattaunawa tsakanin gwamnatin da ƙungiyar da yammacin ranar Laraba.
Lauyan ƴan adaidaita sahun Barista Abba Hikima Fagge ne ya tabbatar da hakan ga Freedom Radio jim kaɗan bayan kammala tattaunawar.
Ya ce, an cimma matsaya ne bayan aka shafe tsawon shafe sa’o’i ana musayar yawu da masu ruwa da tsaki daga bisani a samar da matsaya”.
“Mun tsayar da cewa za a sake zama a ranar 18 ga watan Janairu domin saurarar korafe-korafen yan adaidaita sahu kan hukumar, kuma an cimma matsaya kan cewa hukumar za ta bada guraren fakin a wasu kasuwanni ga direbobin sannan za a dauki mataki kan yan KAROTA da ke cin zarfin direbobin”.
Abba Hikima Fagge ya kuma ce, an cimma matsaya guda 12 a zaman, kuma za a bibiya domin tabbatar da an samu daidaito.
You must be logged in to post a comment Login