Labarai
Dakarun Operation Hadin Kai sun kashe ƴan ta’adda fiye da 50

Shalkwatar tsaron Najeriya, ta ce, dakarun Operation Hadin Kai sun kashe fiye da ƴan ta’adda 50 tare da dakile hare-hare a sansanonin sojoji a jihohin Borno da Yobe.
Rundunar sojin ta ce, yan ta’addan sun kai hare-hare a lokaci guda daga daren jiya Alhamis har zuwa wayewar garin yau Juma’a , inda suka farmaki sansanonin sojoji a Dikwa da Mafa da Gajibo da Katarko waɗanda ke ƙarƙashin sassan 1 da 2 na rundunar hadin gwiwa ta 1.
A wata sanarwa, jami’in yada labarai na rundunar hadin gwiwa ta Arewa maso Gabas Laftanal Kanal Sani Uba, ya ce sojojin sun yi namijin ƙoƙari wajen dakile hare-haren mayakan, inda suka yi wa ƴan ta’adda mummunar asara.
Uba ya ce rundunar ta samu nasarar kashe sama da ƴan ta’adda 50, tare da kwato makamai da dama ciki har da bindigogi AK-47 guda 38, PKT guda 7, makamin gurneti da tarin albarusai.
You must be logged in to post a comment Login