Labarai
Dakarun Operation Safe Heaven sun daƙile harin yan bindiga a Filato

Rundunar sojin Najeriya ta Operation Safe Heaven, ta ce, ta daƙile wani yunkurin kai hari a ƙauyen Teegbe da ke karamar hukumar Bassa ta jihar Filato, tare da kashe ɗaya daga cikin maharan.
Wata sanarwa da mai magana da yawun rundunar Manjo Samson Nantip Zhakom, ya fitar a Alhamis din makon nan, ta ce, lamarin ya faru ne ranar Laraba 23 ga watan nan da muke ciki na Afrilu, inda artabun da sojojin suka yi da maharan ya janyo wasu da cikinsu suka tsere.
Haka kuma, ta cikin sanarwar ya ƙara da cewa dakarun sun kuma samu nasarar kama wasu ƴan fashi uku a wani samame da suka kai hanyar Katnan uwa Buratali da ke yankin Wase.
Rundunar ce an samu mutanen da ake zargin ɗauke da wata bindiga da ake ƙera wa a cikin gida, kuma sun amsa cewa sun yin fashi tare da wasu ƴan uwansu a hanyar.
You must be logged in to post a comment Login