Labarai
Dakarun Soji na Operation Hadin Kai sun kama wadanda ake zargi da taimaka wa Boko Haram

Dakarun sojin Najeriya na rundunar Operation Hadin Kai ta kama wasu da ake zargi da taimaka wa Boko Haram tare da kashe wasu ’yan ta’adda a Jihohin Adamawa da Borno.
Wannan dai na kunshe ne cikin wata sanarwar da Jami’in yada Labarai na rundunar, Sani Uba ya fitar a ranar Alhamis 19 ga Fabrairun da muke ciki.
Sanarwar ta ce a yankin Visik da ke Karamar Hukumar Hong ta Jihar Adamawa, sojoji sun cafke Ismail Muhammed mai shekaru 28 da ake zargin yana samar da kayayyakin tallafi ga ’yan ta’adda, inda aka samu bindiga kirar AK 47 guda daya, harsasai, kayan soji da kayayyakin abinci a hannunsa.
You must be logged in to post a comment Login