Labarai
Dakarun Sojin Najeriya sun hallaka ‘yan bindiga a jihar Borno

Dakarun Sojin Rundunar Operation Haɗin Kai, sun kashe ’yan ta’adda biyu a wani samame da suka kai yankin Shettimari da ke Ƙaramar Hukumar Konduga, a Jihar Borno.
Majiyoyi sun shaida cewa rundunar ta kai harin ne ƙarƙashin Operation Desert Sanity V da safiyar ranar Alhamis.
Tun da fari Sojojin sun tare mayaƙan a kusa da inda suke shirin kai hari a yankin da misalin ƙarfe 1:20 na dare.”
Bugu da ƙari, majiyar ta ce daga baya an gano wasu bama-bamai guda biyu da kuma wani gidan harsashi guda ɗaya mai ɗauke da harsasai 23 da ’yan ta’addan suka watsar yayin da suke tserewa.
Majiyar ta ƙara da cewa, ba’a samu asarar rai daga bangaren sojojinba
You must be logged in to post a comment Login