Labarai
Dakarun sojin Najeriya sun hallaka ‘yan ta’addan ISWAP a jihar Borno

Dakarun rundunar Operation Hadin Kai, da hadin gwiwar ‘yan sa kai sun yi nasarar kashe mayakan ISWAP 17 a wani samame da suka kai da sanyi safiyar Lahadi, a jihar Borno.
Mai magana da yawun rundunar, Laftanal kanal Sani Uba, ya ce sun yi nasarar ne bayan tattara bayanan sirri a kan zirga-zirgar mayakan.
Ya ce dakarun sun tarwatsa maboyar ‘yan ta’addan kungiyar JAS da na ISWAP a kauyukan Sojiri da Kayamla na jihar Borno.
Daga cikin kayan da aka kwato daga hannun mayakan akwai babura da kayan abinci da magunguna da kayan sawa da kuma bindigogi da alburusai kala-kala.
You must be logged in to post a comment Login