Labarai
Dakarun sojin Najeriya sun ragargaza wani sansanin ‘yan bindiga

Dakarun sojin ƙasar nan na rundunar 22 Armoured sun lalata wani sansanin ’yan bindiga a Karamar Hukumar Ifelodun ta Jihar Kwara.
Wannan dai na cikin wata sanarwar da Mataimakiyar Daraktar Hulɗa da Jama’a ta Rundunar, Kyaftin Maureen Ogbuka, ta fitar a ranar Juma’a.
Sanarwar ta bayyana cewa aikin ya gudana ne tsakanin ranar 23 zuwa 29 ga Janairu 2026, inda sojoji suka lalata maboyar ’yan bindiga da sansanoninsu tare da katse hanyoyin da suke amfani da su wajen jigilar kayayyaki.
Ta ƙara da cewa sojojin sun cafke wasu da ake zargi da aikata laifuka, tare da ceto mutanen da aka yi garkuwa da su daga wurare daban-daban a jihar.
Sanarwar ta kuma bayyana ce a yayin samamen, sojojin sun kashe ɗaya daga cikin ’yan bindigar, yayin da wasu suka tsere zuwa daji.
You must be logged in to post a comment Login