Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Daliban Sakandaren Gwale, Aji na 1994, sun cika shekaru 30 da kammala makarantar

Published

on

Kungiyar tsofaffun Daliban makarantar Sakandaren Gwale wato Goba, Aji na Alif 1994 ta bukaci kungiyoyin Dalibai da su rinka yin wani abu da zai ciyar da makarantun da suka kammala gaba.

Shugaban kungiyar Alhaji Bello Danbaffa ne ya bayyana hakan yayin bikin cikar su shekaru 30 da kammala makarantar ta GSS Gwale.

Da yake bayar da tarihin kungiyar Daliban ta Goba a jawabin da ya gabatar shugaban ta na kasa Injiniya Hassan Abdulkadir bayyana Irin gudunmawar da wasu Yayan kungiyar ke baiwa makarantar ya yi.

Haka zalika Taron ya samu halartar shugaban rundunar sojin kasar nan shiyyar Kano Group Kaftin Mustafa Sulaiman, Wanda shima guda ne daga cikin daliban makarantar ta Gwale Aji na Alif 1994.

Kazalika kungiyar ta karrama wasu daga cikin mutanan da suka samu wasu mukamai da Kuma bayar da gudunmawar su a tafiyar kungiyar.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!