Labarai
Dalilaina na rashin komawa majalisa bayan samun umarnin Kotu- Sanata Natasha

Sanata mai wakiltar mazaɓar Kogi ta Tsakiya,Natasha Akpoti-Uduaghan ta bayyana cewa ta jinkirta komawarta majalisa ne sakamakon shawarwarin lauyoyi da kuma bin dokoki, duk da cewa kotu ta soke dakatarwar da aka yi mata.
Ta cikin wata hira da ta yi da gidan talabijin na AIT, Sanata Natasha ta ce tana jiran takardar hukuncin kotu kafin ta ɗauki matakin komawa majalisar.
A baya baya nan kotu ta ce dakatarwar da aka yi mata ta yi yawa kuma ba bisa ƙa’ida aka yi ta ba.
Wani lauya daga Majalisar Dattawa, Paul Daudu mai matsayin (SAN), ya bayyana cewa hukuncin bai ƙunshi umarnin tilasta majalisar ta dawo da ita ba.
Sanarwar dawowarta da aka shirya yi a ranar Talatar da ta gabata ya tayar da hankula a majalisar, inda aka tsaurara tsaro tare da kawo motocin jami’an tsaro da dama.
You must be logged in to post a comment Login