Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labaran Kano

Dangote ya tallafa mana da kayayyakin aiki-‘Yan bijilanti na Kano

Published

on

Shugaban Kungiyar sintiri ta Bijilanti na Jihar Kano Muhammad Kabir Alhaji ya bukaci hamshakin dan kasuwa Alhaji Aliko Dangote daya kawo musu tallafin kayan aiki kamar yadda ya shahara wajen tallafawa rundunar ‘yan Sandan Najeriya , domin sun fi kowa bukatar tallafi.

Muhammad Kabir Alhaji ya bayyana hakan ne lokacin da yake zantawa da wakilin Freedom Radio Abdulkarim Muhammad Abdulkarim Tukuntawa a nan Kano.

Shugaban Kungiyar Muhammad Kabir Alhaji ya ce samun ingantattun kayan aiki zaiyi matukar taimakawa ayyukan kungiyar wajen cigaba da samar da ingantaccen tsaro lungu da sako a jihar Kano.

Kabir Alhaji ya kara da cewa a shekarar da muka yi bankwana da ita ta 2019 kimanin jami’an kungiyar uku aka kashe har Lahira sakamakon tsayawa kai da fata wajen samar da cikakken tsaro a Kano.

Mk Alhaji ya kuma nanata cewa kungiyarsa ta Bijilanti zata cigaba da hadakai da sauran jami’an tsaro domin magance duk wani abu da ka iya yiwa tsaron jihar  Kano barazana.

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!