Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Dattawan Kwankwasiyya ne suka kai ƙara ta wajen Buhari – Ganduje

Published

on

Gwamnatin jihar Kano ta ƙalubalanci wasu cikin dattawan Kano kan matakin da suka ɗauka na kai wa shugaba Muhammadu Buhari ƙorafi kan batun ƙarɓo bashi da gwamnatin Kano ke shirin yin daga kasar China.

Kwamishinan raya karkara na Kano Musa Iliyasu Kwankwaso shi ne ya bayyana hakan ta cikin shirin Kowane Gauta na nan Freedom Radio dake bada damar faɗin albarkacin baki karkashin sashi na talatin da tara na kasar nan.

Kwamishinan ya ce “ku ma janye maganar cewa dattawan jihar Kano ne su ka kai korafin, don kuwa dattawan kwankwasiyya ne kadai”.

Musa Ilyasu ya zargi dattawan da yunkurin hana ci gaban jihar Kano, inda ya ce gwamnati ta tattauna da masana kan batun ciyo bashin domin kuwa abu ne da zai kawo wa Kano ci gaba tare da farfaɗo da tattalin arzikin jihar dama kasa baki daya.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!