Labarai
Ya kamata gwamnati ta sanya hannun jari a kasuwarmu ta Dawanau- Alh. Muttaka Isah
Shugabancin kasuwar hatsi ta Dawanau ya buƙaci haɗin kan ƴan kasuwar gwamnati da kungiyoyi masu zaman kansu wajen ci gaba da samarwa da kasuwar ci gaba, da samar da saukin hauhawar farashi a wannan lokaci da ake ciki.
Shugaban kasuwar Alhaji Muttaka Isah ne yayi wannan jawabin yayin da yake ganawa da manema labarai a ranar Lahadi 17 ga watan Maris 2024.
Alhaji Muttaka Isah ya kuma ce samar da hanyoyin zamani na layin dogo zai taimaka wajen isar kayan masarufi inda ake da buƙata su isah wanda hakan zai rage wannan wahalar kayan abinci.
Wannan matsalar ta hauhawar farashin kayan abinci da ake fuskanta a Wannan lokaci shine muke kira ga gwamnati da ta shigo fannin noma da kasuwancin kayan hatsi wajen zuba jari domin samarwa da al’umma sauki acewar Shugaban kasuwar.
Haka kuma kasuwar Dawanau na ƙoƙarin bayar da gudummawa ga al’ummar da suke a yankin musamman mutanen ƙaramar hukumar Dawakin Tofa wajen bayar da abinci ga al’umma domin rage musu raɗaɗin matsin rayuwa.
Alhaji Muttaka ya kuma ce kasuwar su ta Dawanau ta sami nasarori wajen samar mata da hanyoyin ruwa la’akari da yadda a baya wannan kasuwar take fama da barazanar hanyar ruwa,
Haka kuma mun zauna da babban bankin duniya wajen samar da aiki ga matasan su na cikin kasuwar da samar da tsayayyiyar hutar lantarki a kasuwar.
Dan haka nan da ɗan wani lokaci mutanen kasuwar su zasu fara daukar kayan su zuwa wasu garuruwan ba tare da wani tasgaro ba.
Haka kuma muna ta shirye-shiryen yadda zamu samu alaƙa tsananin mu da jami’an tsaro wajen daƙile tare motocin kayan mu akan hanya ba tare da wani cikakken laifi ba.
Daga ƙarshe shugaban kasuwar ya yabawa gwamnatin Kano bisa irin gudunmawar da take bayarwa ga al’ummar jihar wajen ganin ta samar musu da saukin matsin rayuwa da ake ciki.
You must be logged in to post a comment Login