Labarai
DFID ta baiwa ‘yan jarida horo a Jigawa
Kungiyar shirin lafiya ta jihar Jigawa wacce ke aiki da tallafin hukumar raya kasashe ta Birtaniya (DFID) ta gudanar da horo ga ‘yan jaridar Jihar kan yadda zasu gudanar da ayyukansu na wayar da kai gameda annobar corona virus.
Wakilinmu Ali Rabiu Ali Wanda ya halarci taron ya rawaito cewa taron ya samu halartar ‘yanjaridu daga lafafen yada labarai da na jarida.
Jami’in shirin a Jigawa Abdurahman Idris ya ce, hukumar raya kasashe ta Birtaniya wato DFID ce ta dauki nauyin shirin domin bawa manema labarai horo kan yadda za su rika shirye-shiryensu a fanin yaki da annobar COVID-19.
Abdulrahman yace annobar corona virus gaskiyace kuma na saurin yaduwa ta hanyar taba wani abu ko shakar tarin mai dauke da annobar ko kuma ta hanyar taba wani abu da mai cutar ya taba.
Ya kuma ja hankalin al’umma da su ci gaba da bin hanyoyin kariya wanda hukumomin da alhakin kula da yaduwar cutar ya rataya akansu ke bada shawara.
You must be logged in to post a comment Login