Labarai
Rushewar gine-gine: Dokar bibiyar tsara gine-gine ce ta yi rauni a Kano – KNUPDA
Hukumar tsara birane ta jihar Kano KNUPDA ta alaƙanta raunin dokar da aka samar ta bibiyar gine-ginen da ake yi ba bisa ka’ida ba, a matsayin abinda ke haifar da faduwar gine-gine.
Mataimakin Daraktan hukumar na sashin kula da gine-gine Alhaji Aliyu Yusuf Dada ne ya bayyana hakan ta cikin shirin Barka da Hantsi na Freedom radio.
Dada ya ce yin gini a kan kududdufin da aka cike da shara na haifar da rushewar gine ginen.
“Gini kan kududdufin da aka cike ba matsala bane idan aka bi ka’idoji tare da neman shawarar ƙwararru a fannin gine-gine”.
Aliyu Dada ya ƙara da cewa hukumar ta KNUPDA na zagawa lungu da saƙo na jihar Kano domin dakatar da duk wani gini da aka yi ba bisa ƙa’ida ba.
You must be logged in to post a comment Login