Connect with us

Labarai

Dole ne a kafa ‘Yan-sandan jihohi – Tinubu

Published

on

Shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, ya buƙaci Majalisar Wakilai ta sanya matakan kariya a cikin gyaran kundin tsarin mulki domin kafa ‘yan sandan jiha, ta yadda gwamnoni ba za su iya amfani da su wajen cin zarafi ba.

 

Ya bayyana haka ne a fadar shugaban ƙasa yayin buɗa-baki da ‘yan majalisar, inda ya jaddada cewa tsaro al’amari ne na cikin gida, don haka dole a yi gyaran da zai haɗa da tsarin da ba za a iya amfani da shi ba kamar yadda aka yi a jamhuriya ta farko.

 

Shugaban ya ce dole ne a kafa ‘yan sandan jiha domin tinkarar matsalolin tsaro, amma a yi hakan da tsare-tsare masu ƙarfi. Ya kuma yaba wa ‘yan majalisar kan goyon bayan da suka ba gwamnatinsa kan cire tallafin mai da kuma sassauta darajar naira.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!