Labarai
Dole ne Al’umma su hada kai da hukumar Kashe gobara-Usman Alhaji
Sakataren gwamnatin jihar Kano Alhaji Usman Alhaji ya bukaci jama’a da su rika baiwa jami’an hukumar kashe gobara ta jihar Kano hadin kai a yayin da suke gudanar da aikin suna ceton rayuka da dukiyoyi a lokacin da gobara ta tashi.
Alhaji Usman Alhaji ya wannan jan hankalin ne a lokacin da ake gudanar da taron wayar da kan ‘yan kasuwa wanda ya gudana a hukumar kashe gobara ta jihar Kano.
Ya kara da cewa gwamnati na kokari wajen samawa hukumar kayayyakin aiki masu inganci kuma duk wata kasuwa an samar mata da wata hanya da jami’an kashe gobara zasu shiga domin kashe gobara, idan bukatar hakan ta taso.
Gobara ta tashi a FCE dake Kano
Dorayi-Giza:Gobara ta yi sanadiyar mutuwar wasu iyalai su uku
Wata gobara ta kone dakuna 25 da shaguna 12 a birnin Illorin, jihar Kwara
A nasa jawabin shugaban hukumar kashe gobara na jihar kano inginiya Kazeem Sola Ya ce, Kamata yayi al’umma su kauracewa amfani da wuta domin jin dumi kasancewar yanayin sanyi ya fara nuna alamun shigowa domin gujewa afkuwar gobara.
Shima a nasa bangaren hakimin karamar hukumar Fagge Alhaji Mahmud Ado Bayero yaja hankalin masu hannu da shuni da su rika shiga aikin wajen samar musu da kayayyakin aiki, ba wai sai an rika jiran gwamnati a kowanne lokaci ba.
Wakilin mu Shamsu Dau Abdullahi ya ruwaito cewa, mahalalta taron na kira ga jama’a da su rika kula da kayayyakin wuta.