Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Yadda mutane 3 suka rasa rayukan su sanadiyar tashin gobara a Kano

Published

on

Hukumar kashe gobara ta jihar Kano ta tabbatar da rasuwar muta ne 3 ‘yangida daya a wata gobara da ta tashi a unguwar Rijiyar zaki dake karamar hukumar Ungogo.

Cikin wata sanarwa hukumar ta ce lamarin ya afko ne da misalin karfe 3 da minti 18 na daren jiya a Rumfar Shehu.

Sai dai a  cewar hukumar tana cigaba da gudanar da binciken musabbabin tashin gobarar a halin yanzu

Malam sa’idu Muhammad shi ne kakakin hukumar kashe gobara ta jihar Kano ya ce da misalin karfe 3 na dare da minti 22. ne suka sami kiran gaggawa ta wayoyin su kan cewa an sami tashin gobara a Unguwar Rijiyar zaki dake karamar hukumar Ungogo.

Sai dai Shugaban hukumar Malam Salisu Muhammad ya bayyana cewa da zuwan su ke da wuya sai suka sami wani gida wuta na ci ya yin da kuma mutum 3 sun makale a ciki bayan da jami’an hukumar ta kashe gobarra suka kutsa kai.

Malam Salisu Muhammad ya kuma ce shigar ba jimawa suka sami nasarar ceto mutum 3 in da nan take suka dauke su zuwa asibitn kwararru na Murtala Muhammad  don samun kulawar gaggawa.

Amma daga bsani sai hukumomin asibitin suka tabbatar musu  cewar mutanen sun riga mu gidan gaskiya

Shugaban hukumar ta kashe gobara ya ce  hukumar zata cigaban da gudanar da  binciken kan musababin tashin gobarar.

 

 

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!