Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Dole ne Al’umma su hada kai da hukumar Kashe gobara-Usman Alhaji

Published

on

Sakataren gwamnatin jihar Kano Alhaji Usman Alhaji ya  bukaci jama’a da su rika baiwa jami’an hukumar kashe gobara ta jihar Kano hadin kai a yayin da suke gudanar da aikin suna ceton rayuka da dukiyoyi a lokacin da gobara ta tashi.

Alhaji Usman Alhaji ya wannan jan hankalin ne a lokacin da ake gudanar da taron wayar da kan ‘yan kasuwa wanda ya gudana a hukumar kashe gobara ta jihar Kano.

Ya kara da cewa gwamnati na kokari wajen samawa hukumar kayayyakin aiki masu inganci kuma duk wata kasuwa an samar mata da wata hanya da jami’an kashe gobara zasu shiga domin kashe gobara, idan bukatar hakan ta taso.

Gobara ta tashi a FCE dake Kano

Dorayi-Giza:Gobara ta yi sanadiyar mutuwar wasu iyalai su uku

Wata gobara ta kone dakuna 25 da shaguna 12 a birnin Illorin, jihar Kwara

A nasa jawabin shugaban hukumar kashe gobara na jihar kano  inginiya Kazeem Sola Ya ce, Kamata yayi al’umma su kauracewa amfani da wuta domin jin dumi kasancewar yanayin sanyi ya fara nuna alamun shigowa domin gujewa afkuwar gobara.

Shima a nasa bangaren hakimin karamar hukumar Fagge Alhaji Mahmud Ado Bayero yaja hankalin masu hannu da shuni da su rika shiga aikin wajen samar musu da kayayyakin aiki, ba wai sai an rika jiran gwamnati a kowanne lokaci ba.

Wakilin mu Shamsu Dau Abdullahi ya ruwaito cewa, mahalalta taron na kira ga jama’a da su rika kula da kayayyakin wuta.

 

 

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!