Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Dole ne mulki ya koma kudu: Shin ina makomar takarar Atiku, Kwankwaso da Tambuwal?

Published

on

A wata sanarwar bayan taro da ƙungiyar gwamnonin kudancin ƙasar nan su ka fitar a baya-bayan nan ta fito da buƙatun da ke neman al’ummar Najeriya baki ɗaya da su goyi bayan ɗan takarar shugaban ƙasa a zaɓen shekara ta 2023 ya fito daga kudancin ƙasar nan.

 

Sanarwar bayan taron mai ɗauke da sa hannun shugaban ƙungiyar gwamnonin na kudu Rotimi Akeredolu na jihar Ondo, ta ce, wajibi ne jam’iyyun Najeriya su yi amfani da tsarin karɓa-karɓa wajern fitar da ɗan takarar da zai shugabanci ƙasar nan a shekarar 2023.

 

Wannan matsaya ta gwamnonin na kudu na zuwa ne a lokaci guda da wasu ƴan siyasa a jihohin arewa ciki har da wasu daga cikin gwamnoni ke zawarcin kujerar ta shugaban ƙasa a shekara ta 2023 duk da cewa shugaba mai ci Muhammadu Buhari ya fito ne daga yankin na arewa.

 

Waɗanda ke kan gaba cikin masu fafutukar neman kujerar shugaban ƙasar a shekarar 2023 daga yankin arewa sun haɗa da: tsohon mataimakin shugaban ƙasa Alhaji Atiku Abubakar da tsohon gwamnan jihar Kano Dr. Rab’iu Musa Kwankwaso da kuma gwamnan jihar Sokoto Aminu Waziri Tambuwal.

 

Sauran sune: Gwamnan jihar Kogi Yahya Bello da tsohon gwamnan jihar Zamfara sanata Ahmed Sani Yariman Bakura da gwamnan jihar Bauchi sanata Bala Abdulƙadir Muhammed.

 

Ko da ya ke siyasa ba ta tabbas, tana iya sauyawa a kowane lokaci, amma ba ko shakka wannan matsaya da gwamnonin na kudanci da suka ɗauka zai sanya waɗannan zaurawa na arewa zaman zullumi domin kuwa burinsu na ɗarewa akan kujera ta ɗaya mafi daraja a Najeriya tana ƙasa tana dabo.

 

To koma me zai faru Allah ne masani, lokaci kawai ake jira.

 

 

 

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!