Labaran Kano
Dr Sani Malumfashi:rashin shugabanci nagari na haifa da rashin amana tsakanin al’umma
Wani malami a sashen nazarin zamantakewar dan adam a Jami’ar Bayero da ke nan Kano Farfesa Dr Sani Malumfashi ya bayyana rashin shugabanci nagari a kasar nan a matsayin abinda ke kara haifar da karancin amana da gaskiya a tsakanin alu’mma.
Farfesa Sani Lawan ya bayyana hakan ne yau jim kadan bayan kammala shirin Barka da Hantsi na nan Freedom Rediyo.
Ya kuma kara da cewa al’amarin ya kara ta’azzara ne sakamakon rashin huunta masu rike da mukaman gwmanati da ake kamawa da laifin cin amana tare da kuma da baiwa wadanda ba su cancanta ba mukamai. mukamai.
A na sa bangaren limanin Masallacin Ibn Taimiyya da ke Unguwar Na’ibawa a nan Kano, Malam Imam Muhammad Nuhu, cewa ya yi karancin gskiya da rikon ama ne ya jefa al’umma cikin wannan yanayi na kunci a halin yanzu.
Malamin ya shawarci iyaye su jajirce wajen tarbiyyantar da ‘ya’yansu tare da nuna mu su illar da rashin gaskiya da cin amana ke haifarwa.