Labarai
Dukkan wanda hukuncin da kotun daukaka kara ya shafa kan masarautar Kano ya yi biyayya – Dederi
Gwamnatin jihar Kano ta bukaci dukkan wanda hukuncin da kotun daukaka kara ya shafa kan masarautun jihar da ya tabbatar da ya yi biyayya ga umarnin Kotun.
Kwamishinan Shari’a na jihar kuma Antoney Genel Haruna Isah Dederi ne ya bayyana hakan a zantawarsa da manema labarai kan hukuncin da kotun ta yi na masarautar Kano.
Ya kuma ce wajibi ne dukkanin hukumomi da dukkan wani mutun yabi umarnin hukuncin da kotun daukaka karar ta zartar.
Dederi ya kuma yabawa fannin shari’a kan hukuncin da ta zartar na rushe hukunce hukuncen da kotunan baya suka zartar.
Ya kuma ce hakan na nuni da cewar dokar da majalisar dokokin kano ta zartar na rusa masarautun na Kano ta samu karbuwa.
A ranar juma’a 10 ga watan Janairu ne kotun Daukaka kara ta zartar da hukunci rusa duk hukunce hukuncin da babbar kotun tarayya dake zamanta a nan Kano ta zartar.
You must be logged in to post a comment Login