Labarai
EFCC ta bada belin Ambasada Aminu Wali da Malam Ibrahim Shekarau
Hukumar EFCC ta bayar da belin tsohon ministan harkokin waje Ambasada Aminu Wali, da Tsohon Gwamnan Jihar Kano Malam Ibrahim Shekarau da kuma tsohon kwamishina a jahar Kano Injinya Mansur Ahmad.
Haka zalika bayan bayar da belin nasu, kotu zata rika gayyatarsu duk lokacin da ake bukatarsu.
Ana zargin mutanen 3 ne da karbar tsabar kudade Naira miliyan 950 lokacin mulkin tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan domin yakin neman zabe.
Yanzu haka dai Bayan sun dauki wasu awanni a ofishin hukumar ta EFCC shiyyar Kano sun amsa wasu tambayoyi, a watan Mayun shekarar 2016 ne hukumar ta EFCC ta gayyaci Tsofaffin Ministocin Gwamnatin tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan Ambasada Aminu Wali da Malam Ibrahim Shekarau wanda shima tsohon Minstan Ilimi ne a Gwamnatin shugaba Goodluck Jonathan.
A kwanakin baya dai tsohon Gwamnan Jihar Kano Malam Ibrahim shekarau da aka raba kudin a gidansa ya ce bashi da masaniyar lokacin da aka raba kudaden yakin neman zaben.