Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

EFCC ta bada belin Ambasada Aminu Wali da Malam Ibrahim Shekarau

Published

on

Hukumar EFCC ta bayar da belin tsohon ministan harkokin waje Ambasada Aminu Wali, da Tsohon Gwamnan Jihar Kano Malam Ibrahim Shekarau  da kuma tsohon kwamishina a jahar Kano Injinya Mansur  Ahmad.

Haka zalika bayan bayar da belin nasu, kotu zata rika gayyatarsu duk lokacin da ake bukatarsu.

Ana zargin mutanen 3 ne da karbar tsabar kudade Naira miliyan 950 lokacin mulkin tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan domin yakin neman zabe.

Yanzu haka dai Bayan sun dauki wasu awanni a ofishin hukumar ta EFCC shiyyar Kano sun amsa wasu tambayoyi, a watan Mayun shekarar 2016 ne hukumar ta EFCC ta gayyaci Tsofaffin Ministocin Gwamnatin tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan Ambasada Aminu Wali da Malam Ibrahim Shekarau wanda shima tsohon Minstan Ilimi ne a Gwamnatin shugaba Goodluck Jonathan.

A kwanakin baya dai tsohon Gwamnan Jihar Kano Malam Ibrahim shekarau da aka raba kudin a gidansa ya ce bashi da masaniyar lokacin da aka raba kudaden yakin neman zaben.

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!