Labarai
EFCC ta gurfanar da Abubakar Malami da matarsa da dansa a Kotu

Hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta EFCC, ta gurfanar da Tsohon Ministan shari’a Abubakar Malami da matarsa da kuma dansa a gaban kotu bisa tuhumarsu kan almundahanar makudan kudade.
Da safiyar yau Talata ne dai hukumar ta gurfanar da Abubakar Malami da iyalan nasa bisa zargin almundahanar kudi kimanin Naira biliyan 8 da miliyan 700.
Haka kuma hukumar ta EFCC, ta gabatar da su ne a kotun karkashin jagorancin mai shari’a Emeka Nwite bisa wasu tuhume-tuhume guda 16.
You must be logged in to post a comment Login