Labarai
EFCC ta kwato dukiyar fiye da biliyan 500 cikin shekaru biyu- Shettima

Mataimakin Shugaban kasa, Kashim Shettima, ya bayyana cewa, Hukumar yaƙi da masu yi wa tattalin arzikin kasa ta’annati EFCC, ta samu nasarar tara dukiyar da ta haura ta Naira biliyan 500 a tsawon shekaru biyu na gwamnatinsu.
Shettima, wanda ya wakilci Shugaba Bola Tinubu, ya bayyana haka ne a yayin wani taron bita da ƙara wa juna sani na alƙalai da Hukumar EFCC tare da haɗin gwiwar Hukumar Shari’a ta Najeriya NJC suka shirya a birnin tarayya Abuja.
Haka kuma, Kashim Shettima, ya buƙaci alƙalai da sauran ma’aikatan ɓangaren shari’a da su ƙara ƙaimi tare da yin aiki bisa gaskiya da adalci.
Ya kuma yi gargaɗin cewa ana fara samun matsala ne a ƙasa da zarar masu riƙe da amanar hukunci sun fara tauye haƙƙin masu haƙƙi.
You must be logged in to post a comment Login