Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Kiwon Lafiya

EFCC:ta sake gurfanar da Babachir Lawal tare da wasu mutane uku

Published

on

Hukumar EFCC ta sake gurfanar da tsohon sakataren gwamnatin tarayya Babachir Lawal tare da wasu mutane uku gaban kotun tarayya da ke birinin tarayya Abuja.

Hukumar ta gurfanar da shi ne tare da kanin sa Hamid Lawal da Sulaiman Abubakar da kuma Apeh Monday, sai kuma wasu kanfani guda biyu da suka hadar sa Rholavision da kuma Josmon Technologies.

Hukumar dai ta gurfanar da su ne bisa wasu sabbin laifuka guda goma da suka hadar da halasta kudin haramun, karkatar da kudade zuwa inda basu kamata ba da hadi n baki wajen yin danfarar kudaden da suka tasamma naira biliyan dari biyar.

A baya dai hukumar ta EFCC ta gurfanar da su gaban mai shari’a Okeke a ranar 13 ga watan Fabrairun da ya gabata, inda kuma mai shari’ar ya sanya jiya domin ci gaba da hukuncin. Yayin da aka dawo zaman kotun a jiya lauyan hukumar ta EFCC ya shaidawa kotun cewa hukumar ta sabun ya tuhumar da ake yiwa babachir din da sauran a bokan tuhumar sa

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!