Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Kiwon Lafiya

Bauchi:jam’iyyar APC ta ce zata amince da bayyana sakamakon zaben ba

Published

on

Yayin da hukumar zaben ta kasa INEC ke haramar bayyana sakamanon zaben gwamnan jahar Bauchi a yau Talata bayan tsame jahar daga jerin jahohin da ta ayyana zabukansu a matsayin wanda bai ita kuwa jam’iyyar APC ta ce ba za ta amince da hakan ba.

Jam’iyyar ta APC ta ce ba za ta amince da sauya matsayi da hukumar zabe ta yi na amincewa da ingancin sakamakon zaben Karamar Hukumar Tafawa Balewa a Jahar ba.

A cewar ta, akwai wasu tambayoyi da dama da ya kamata Kwamitin Bincike da INEC ta kafa a karkashin jami’inta, Festus Okoye, ya amsa kafin a dau wannan mataki wanda, a cewarta, mayar da hannun agogo baya ne, kuma Hukumar INEC ba ta da hurumin yin amai ta lashe irin haka.

Wata mamban Kwamitin Yakin Neman Zabe jam’iyyar APC  Hajiya Rabi Sulu Gambari ta ce ba a yi wa APC adalci ba domin ai sakamakon zaben an ce an yaga shi, a cewar ta da wane za a yi amfani wajen fadar sakamakon a yau.

A don haka jam’iyyar APC ta  cd ko kusa ko alama ba za ta amince a ayyana sakamakon zaben Gwamnan a yau ba, illa iya ka bukatar su shi ne a sake zaben a wuraren da basu kammala ba kamar sauran jihohi.

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!