Connect with us

Labarai

Eti-Osa: rikicin kabilanci ya raunata tare da hallaka wasu da ba’a san adadinsu ba

Published

on

Wasu mutane da ba a kai ga sanin adadinsu ba sun mutu wasu jikkata sakamakon wani rikicin kabilanci a yankin Ajah a karamar hukumar Eti-Osa a Jihar Lagos.

Rahotanni sun nuna cewa rikicin ya samo tushe ne kusan makonni biyu da suka bayan da wasu matasan yankin Ilaje suka gwabza fada da takwarorinsu na Ajah kuma aka raunata mutane da dama.

Wasu al’ummar yankin sun shaida cewa batun mallakar wani yanki ne a wurin ya haddasa rikicin, kuma shi kansa Kwamishinan yan sadan Jihar Zubairu Mu’azu ya ziyarci yankin da lamarin ya faru a karshen makon jiya.

Jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jiar Lagos din Bala Elkana ya tabbatar da ziyarar kwamishinan kuma jagororin al’ummar yankin sun yi farin ciki da zuwansa, inda ya yi alkawarin daidaita al’amura garin tare da tabbatar da zaman lafiya

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Freedom Radio Dutse 99.5 FM Dala FM Kano 88.5

Now Streaming

Subscribe to Freedom Radio via Email

Enter your email address to subscribe to this site and receive notifications of new posts by email.

Join 338,336 other subscribers.

Copyright © 2019. Freedom Radio Group. All Rights Reserved.

error: Content is protected !!