Connect with us

Labarai

Fadar Shugaban Kasa ta musanta zargin yunkurin sanya guba wa Tinubu

Published

on

Fadar Shugaban Kasa ta karyata rahotannin da ke yawo a kafafen sada zumunta da ke zargin cewa an kama wasu ma’aikatan girki a Fadar Aso Rock bisa zargin yunkurin sanya guba wa Shugaban Kasa, Bola Ahmed Tinubu.

Mai Bai wa Shugaban Kasa Shawara kan Yada Labarai da Dabaru, Bayo Onanuga, ya bayyana hakan ta shafinsa na X inda ya wallafa bidiyon rahoton tare da yin karin haske cewa labarin ba shi da tushe balle makama. A cewarsa, babu wani ma’aikacin girki da aka kama, kuma babu wani yunkuri na guba wa shugaban kasar.

 

Bidiyon da ake yadawa ya nuna wasu motsi a harabar fadar shugaban kasa tare da muryar da ke cewa an kama wani chef bisa zargin shirin guba wa shugaban kasa, lamarin da ya sa jami’an tsaro suka tsaurara matakan kariya. Sai dai Onanuga ya ce wannan rahoto karya ne tsagwaronsa, yana mai kira ga jama’a da su yi watsi da shi.

 

Fadar Shugaban Kasa ba ta bayar da karin bayani kan asalin bidiyon ko dalilin da ya sa aka kirkiri rahoton ba, amma ta jaddada cewa babu wani barazana da ta shafi lafiyar shugaban kasar.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!