Connect with us

Labarai

Fadar shugaban kasa tayi magana kan sace hakimin Daura kuma sarkin dogarin Buhari

Published

on

Fadar shugaban kasa ta ce sace hakimin Daura kuma sirikin dogarin Buhari ya nuna cewa jami’an tsaro ba sa baiwa wani yanki kulawa ta musamman a kan wani bangare a fadin kasar nan.

Mai baiwa shugaban kasa shawara na kan kafafen yada labarai malam Garba Shehu ne ya sanar da hakan cikin wata sanarwa da ya fitar yau a birnin tarayya Abuja.

Ya kuma ce tuni kwamishinan yan sandan jihar Katsina Sunusi Buba ya koma zuwa birinin Daura domon ganun cewar an kubutar da hakimin daga hannun masu satar mutanen.

Ya kuma ce sace hakimin ya nunawa al’ummar kasar nan cewa matsalar garkuwa da mutane matsalace ta kasa baki daya, a cewar sa ba bu inda ake baiwa kulawa da musamman aka kuma kyale wasu.

Haka kuma ya ce wannan al’amari ya fi karfin ayyukan bata gari, a cewar sa matsala ce ta kasa baki daya da ya kamata a hada hannu wajen magance ta baki daya.

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Freedom Radio Dutse 99.5 FM Dala FM Kano 88.5

Now Streaming

Subscribe to Freedom Radio via Email

Enter your email address to subscribe to this site and receive notifications of new posts by email.

Join 340,482 other subscribers.

Copyright © 2019. Freedom Radio Group. All Rights Reserved.

error: Content is protected !!