Connect with us

Kiwon Lafiya

EFCC ta kwato kadarori 214 a hannun ‘yan siyasa da jami’an gwamnati

Published

on

Hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta EFCC ta ce tsakanin shekarar 2015 shekarar bara, ta kwato kadarori guda dari biyu da goma sha hudu daga wajen jami’an gwamnati da ‘yan siyasa.

A cewar hukumar ta kwato kadarorin ne a jihohin Lagos da Kaduna da Katsina da Jigawa da Kogi da Adamawa da Oyo da kuma birnin tarayya Abuja.

Cikin kadarorin da hukumar ta sanar, har da rukunin gidaje wadanda aka kwace daga wajen wasu mutane 70 da kuma kamfanoni guda 7.

Bayanan kididdigar kadarorin ta nuna cewa, guda 179 an kwace su ne ta hanyar hukuncin kotu na wucin gadi.

Wasu daga cikin wadanda hukumar ta kwace kadarorin su, sun hada da: tsohon mai bai wa shugaba Goodluck Jonathan shawara kan harkokin yada labarai Ima Niboro da tsohuwar ministar Man fetur Diezani Alison-Madueke da tsohon mai bai wa shugaban kasa shawara kan harkokin tsaro kanal Sambo Dasuki mai ritaya.

Haka zalika hukumar ta EFCC ta kuma kwace kadarorin tsohon minista Iyorchia Ayu da tsohon babban hafsan tsaro marigayi Air Marshal Alex Badeh da kuma tsohon babban hafsan sojojin sama Air Marshal Adesola Amosu mai ritaya.

Sauran sune: tsohon gwamnan jihar Ekiti Ayodele Fayose da tsohon gwaman jihar Bauchi Isah Yuguda da kanal Bello Fadile mai ritaya da tsofaffin gwamnonin jihohin Niger da Katsina Babangida Aliyu da kuma Ibrahim Shema

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Freedom Radio Dutse 99.5 FM Dala FM Kano 88.5

Now Streaming

Subscribe to Freedom Radio via Email

Enter your email address to subscribe to this site and receive notifications of new posts by email.

Join 340,925 other subscribers.

Copyright © 2019. Freedom Radio Group. All Rights Reserved.

error: Content is protected !!