Barka Da Hantsi
Fannin ilimi na fuskantar karancin kayan koyo da koyarwa a Kano – NUT
Kungiyar malamai ta kasa NUT reshen jihar Kano, ta bayyana rashin ciyar da malaman gaba da kuma karancin kayan koyo da koyarwa, a matsayin babban kalubalen da fannin ilimi ke fuskanta a nan Kano.
Shugaban kungiyar reshen jihar Kano Malam Hambali Muhammad ne ya bayyana hakan, jim kadan bayan kammala shirin Barka da Hantsi na nan Freedom Rediyo.
Shirin na wannan rana ya mayar da hankali ne kan muhimmancin malaman makaranta a cikin al’umma, da kuma duba dalilai da suka janyo malaman ke rayuwar ƙasƙanci kuma ilimin baya samun inganci.
Malam Hambali Muhammad ya kara da cewa yanzu haka ana samun cunkoson dalibai a cikin azuzuwa tun bayan da gwamnatin jiha ta ayyana kudurin nan na ilimi kyauta kuma wajibi.
You must be logged in to post a comment Login