Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Kasuwanci

Farashin shinkafa ya fadi warwas a Najeriya – Emefiele

Published

on

Gwamnan babban bankin kasa (CBN) Godwin Emefiele, ya ce, farashin buhun shinkafa ya fadi a kasuwannin Najeriya a bana idan aka kwatanta da shekarar da ta gabata lokacin da ake fama da cutar covid-19.

Ya kuma alakanta faduwar farashin buhun shinkfar mai nauyin kilo hamsin da irin tallafi da bankin na CBN ke bayarwa a bangaren noman shinkafa.

Mista Emefiele ya bayyana hakan ne yayin zantawa da manema labarai a ranar talata a Abuja.

Ya ce, farashin shinkfa ya tashi a bara ne saboda matsalar cutar corona sannan a bangare guda gwamnatoci sun saye dan wanda ya rage su ka rabawa jama’a.

Gwamnan na CBN ya kuma shawarci manoma da su karkatar da akalarsu zuwa noman rani wanda hakan zai taimaka gaya wajen samar da isasshen abinci ga kasar nan.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!