Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Biliyan 50 kacal Ganduje zai ciyo bashi amma Kano ta hargitse da hayaniya – Chidari

Published

on

Shugaban majalisar dokokin jihar Kano Injiniya Hamisu Ibrahim Chidari ya ce ya yi mamaki yadda al’ummar jihar Kano suka mai da martani kan batun ciyo bashin naira biliyan hamsin da gwamnatin Dr Abdullahi Umar Ganduje ta yi yunkurin ciyo wa.

A zantawar sa da gidan radio freedom jim kadan bayan kammala shirin ‘barka da hantsi’ Hamisu Ibrahim Chidari ya ce manufar ciyo bashin ita ce rage wa gwamnati radadi sakamakon halin da tattalin arziki ya shiga sanadiyar cutar Corona.

“Jigohi da dama na kasar nan sun ciyo bashin nan”

“Jihar Kaduna za ku ga ana ta ayyukan tituna to ai da kudin bashin da su ka ciyo ne wanda ya kai naira biliyan dari da ashirin”

 

“Su ma jihar Jigawa sun ciyo biliyan tamanin, mune nan Kano kawai muka bukaci miliyan hamsin, kuma duk da haka da batun ya zo gaban majalisa sai muka rage ya dawo biliyan ashirin”.

“Jihar Katsina da sauran jihohi da dama duk an ciyo bashin nan, amma mu nan Kano da batun ya tashi sai gari ya rude kay ya kay ya! Saboda haka ni ina ga don an ciyo bashin biliyan ashirin don gudanar da ayyukan al’umma/ayyukan raya kasa to wannan ba laifi bane” a cewar Chidari

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!