Connect with us

Labarai

Fasinjoji 26 ne suka samu raunika a hatsarin jirgin ƙasan Kaduna zuwa Abuja- NRC

Published

on

Hukumar lura da sufurin jiragen kasa ta kasa NRC ta tabbatar da cewar fasinjoji 26 ne suka samu raunuka sakamakon hatsarin jirgin ƙasan da ya faru hanyar Kaduna zuwa Abuja a jiya Litinin.

 

Hukumar, ta bayyana hakan ne ta cikin wata sanarwa da ta fitar a safiyar yau Talata a shafinta na X.

 

Haka kuma hukumar ta NRC, ta bayyana cewa baya ga fasinjojin da suka samu raunika akwai wasu daga cikin ma’aikatan jirgin da suka ji rauni

 

Sanarwar ta ce, shugaban hukumar, Kayode Opeifa, ya ce, hatsarin ya faru ne da misalin ƙarfe 9:16 na safe kusa da tashar Asham, inda aka ji ƙara mai ƙarfi lokacin da wani ɓangare na jirgin ya yi karo.

 

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!