Labarai
FCET Bichi na shirin fara karatun Digiri na ƙashin kanta

Kwalejin ilimi da fasaha ta gwamnatin tarayya da ke garin Bichi a Kano, zata fara koyar da karatun Digiri na kashin kanta ba tare da haɗin gwiwa da kowacce jami’a ba.
Shugaban kwalejin fasahar ta Bichi dakta Bashir Sabo Abubakar, ne ya bayyana hakan jim kadan bayan da tawagar gwamnatin tarayya karkashin hukumar da ke kula da jami’o’i Najeriya NUC suka kai ziyarar duba kayan aiki da malamai don sahale wa kwalejin fara yin karatun Digirin.
Dakta Bashir Sabo, ya kuma ce, ya na da kwarin gwiwar yin nasara wajen samar wa da al’ummar jihar kano ingantatcen ilimi idan hukumar ta sahale musu fara gudanar da karatun na Digiri.
You must be logged in to post a comment Login