Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Kasuwanci

FIRS: Ma’aikatar bunkasa masana’antu tayi hasashen tara naira biliya 1 daga wani sashenta

Published

on

Ma’aikatar Bunkasa Masana’antu da kasuwanci da Zuba Jari ta Najeriya ta yi hasashen samar wa gwamnatin tarayya da kudaden shiga Naira biliyan 1 daga ayyukan sashinta na gwaji da awon kayayyaki a shekarar 2021.

Daraktan Sashen, Hassan Tai Ejibunu ne ya bayyana hakan yayin da yake jawabi a taron ma’aikatan gudanarwar sashen a Abuja.

Ya kuma ce, ko a watan Yulin da ya gabata sashen ya tara wa gwamnatin tarayya kudi sama da naira miliyan 357.

Ya ce, hakan na zuwa ne bisa umarnin da gwamnatin tarayya ta bawa ma’aikatar don inganta kokarin da take yi na samar da kudaden shiga kafin karshen wannan shekarar ta 2021.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!