Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

NBC na tuhumar Channels TV da saɓa doka

Published

on

Hukumar kula da kafafen yada labarai ta kasa ta aikewa da gidan talabijin na Channels takardar tuhuma.

Wannan ya biyo bayan wasu kalamai da gwamnan jihar Benue Samuel Ortom yayi a wani shirin safe da suke gabatarwa.

Hukumar ta bayyana hakan ta cikin takardar tuhumar da ta aikewa gidan talabijin din a yau, mai ɗauke da sa hannun shugaban ta Balarabe Ilelah.

NBC ta ce, gidan talabijin din ya saɓa ka’idar aiki, sakamakon yadda ya bar gwamnan ya yi wasu kalaman tunzuri wadanda ba su kamata ba a ranar Talatar da ta gabata.

A don haka hukumar ta buƙaci gidan Talabijin na Channels yayi bayanin dalilin da yasa bai yi amfani da dokokin yaɗa labarai da suka dace ba, wajen gabatar da shirin.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!