Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Fitaccen malamin addinin Musulunci a Kano Sheikh Ahmad Bamba ya rasu

Published

on

*Fitaccen malamin addinin Muslunci a Kano Sheikh Ahmad Bamba ya rasu

Allah ya yi wa babban malamin addinin Musulunci a Kano Sheikh Ahmad Bamba “Ƙala Haddasana” ya rasu.

Malamin ya rasu ne bayan gajeriyar rashin lafiya, a Asibitin koyarwa na Malam Aminu Kano.

Guda daga cikin ƴaƴansa mai suna Rukayya Ahmad ta tabbatar wa da Freedom Radio rasuwarsa.

Ta ce, za a yi jana’izar sa bayan sallar juma’a a masallacin Darul-Hadith.

Fitaccen malamin ya yi fice ne a fagen wajen karatuttukan Hadisi, wanda a baya yake karantarwar a Masallacin BUK, yayin da daga baya ya bude majalisinsa na Darul Hadis.

Muna addu’ar Allah ya jiƙansa.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!