Labarai
Fiye da mutane Miliyan 2 ne kadai suka kammala yin rajistar zabe ta Internet- INEC

Hukumar zaɓe ta kasa INEC ta ce daga cikin al’ummar kasar sama da miliyan 9 da suka fara yin rijistar katin zaɓe ta intanet, sama da miliyan 2 ne kawai suka kammala cika rajistar.
Hakan na kunshe a cikin sanarwar da mai magana da yawun hukumar Uwargida Victoria Eta-Messi, ta fitar da aka rabawa manema labarai.
Jami’ar ta ce jihar Osun ce kan gaba da ta fi kowa yawan sabbin masu rijista da lamba 200,251, sai jihar Kano da 151,604, kana Imo da 144,912 da kuma Sokoto da 141,526.
Jihohin da suka fi ƙaranci masu rijista sun haɗa da Ekiti da Abia da Ondo da Enugu da Ebonyi.
Hukumar ta INEC da masu sanya ido sun ce babban giɓin da ake samu na rashin cike rijistar shi ne mutane da dama na fara rijista amma ba sa samun damar kammala ɗaukar hoto da sauran bayanai.
You must be logged in to post a comment Login