Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Freedom Radio na alhinin rashin Abdullahi Garba Baji

Published

on

Da safiyar yau ne aka yi jana’izar Garkuwan Matasan Tudunwada Alhaji Abdullahi Garba Baji, ɗaya daga cikin ma’aikatan Freedom Radio.

Marigayin ya rasu da asubahin yau Juma’a, bayan fama da rashin lafiya.

Abdullahi Baji na cikin ma’aikatan farko-farko a sashen tallace-tallace na tashoshin Freedom Radio da Dala FM.

Da yake bayyana alhininsa kan wannan rashi, Shugaban sashen talla na Freedom Radiyo, Alhaji Aminu Bello ya ce wannan babban rashi ne aka yi.

Ya ci gaba da cewa “Baji yana daga cikin waɗanda suka fara aiki a sashen kasuwanci na Freedom Radio kuma yana ɗaya daga cikin wadanda suka kawowa sashen ci gaba”.

“Marigayin mutumin kirki ne yana zaune lafiya da abokan aikinsa ba shi da hayaniya kuma baya fushi”.

An yi jana’izar Abdullahi Garba Baji a gidansa da ke Tagarji a unguwar Rimin Keɓe a yankin ƙaramar hukumar Nassarawa.

Marigayin ya rasu ya bar mahaifiyarsa, da matar da ƴaƴa da kuma ƴan uwa.

Yanzu haka tun al’umma da ɗaiɗaikun mutane ke ta bayyana alhininsu jan rashin marigayin, inda hotunansa ya karaɗe kafafen sada zumunta.

Ƙungiyoyi da sauran jama’a na ci gaba da aike wa Freedom Radio saƙon ta’aziyya.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!