Connect with us

Labarai

Freedom Radio za ta buga wasan sada zumunci da Road Safety

Published

on

A yammacin yau ne za a fafata wasan sada zumunci tsakanin ‘yan wasan Freedom Radio da na Hukumar Kiyaye Aukuwar Hadura ta jihar Kano wato Road Safety, a wani bangare na wasanni da ake bugawa don kara zumunci tsakanin ma’aikatu.

Za dai a fafata wasanni da misalin karfe 4 na yamma a filin wasa na Freedom Arena dake harabar gidan Radio Freedom.

Da yake zantawa da manema labarai, Kyaftin din Freedom Radio Nura Bello Wato BelNur ya bayyana cewa yana da kwarin guyiwar zasu samu nasara a wannan wasan da ci 4 da nema.

Yayin da mai horas da ‘yan wasan na Freedom Radio Tijjani Adamu ya ce sun shirya tsaf don samun nasara.

A nasa bangaren alkalin da zai busa wannan wasan Tijjani Abubakar Alfindiki yayi alkawarin yin adalci a yayin jagorantar wasan.

‘yan wasan da zasu wakilci Freedom Radio sun hada da

Nasir Salisu Zango

Salisu Baffayo

Nura Bello (BelNur)

Muzammil Ibrahim Yakasai

Engr. Zahraddin Usman Said

Da dai sauran ma’aikatan Freedom Radio.

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Freedom Radio Dutse 99.5 FM Dala FM Kano 88.5

Now Streaming

Archives

Copyright © 2019. Freedom Radio Group. All Rights Reserved.

error: Content is protected !!